1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Pakistan ta amince da takarar tsohon Firaminista Nawaz

Zainab Mohammed Abubakar
December 28, 2023

Hukumar zaben Pakistan ta amince da takarar tsohon Firaminista Nawaz Sharif a zaben shekarar 2024, makonni bayan da wata kotu ta yi watsi da wasu laifuka biyu na cin hanci da rashawa.

Hoto: Ali Kaifee/DW

Sai dai har yanzu Sharifna bukatar a cire masa dokar da ta haramta masa rike duk wani mukami na gwamnati domin ya cancanci tsayawa takara, don haka ba a bayyana yadda aka amince da bashi damar yin takarara ba.

A shekarar 2017 ne dai kotun kolin Pakistan ta dakatar da Sharif shiga zabe, saboda dalilai na rashin gaskiya wajen bayyana yawan kudaden shigar wani kamfani mallakar dansa.

Sharif, wanda ya dawo gida a watan Oktoba dagagudun hijirar-kashin-kaina tsawon shekaru hudu a London, yana neman tsayawa takara karo na hudu a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Fabrairu.