Nazari game da dambaruwar siyasar Nijar
February 11, 2014Talla
A wannan Talatar (11. 02. 2014) ce, kotun kolin karya shari'a a Jamhuriyar Nijar, wato Cour de Cassation, ta sake zaman shari'ar rikicin jam'iyar CDS Rahama da ke adawa, tsakanin ministan albakatun Gona Abdu Labo, da shugaban jami'yar Mahaman Usman.
Wannan takaddamar ta ake kunno kai ne a yayin da batun kudaden da tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou ya bari bayan kifar da mulki, ke ci gaba da daukar hankalin jama'a, inda tsohon shugaban kasar ya baiyana bankin raya kasashen Musulmi ya taimaka ma Nijar don gudanar da aikin babban Dam, wato Marage Candaji.
Mawallafi : Mamman Kanta
Edita : Saleh Umar Saleh