1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari game da yake-yake a Mali da Siriya

February 4, 2013

Kungiyar kasashen Musulmi za ta tattauna rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a Mali da Siriya a birnin alQahiran Masar.

Islamic countries' leaders pose for official photos before an extraordinary session of the Organization of Islamic Conference in Mecca, Saudi Arabia, Tuesday, Aug. 14, 2012. Saudi Arabia’s King Abdullah hosted the conference, a body of 57 member states, which agreed to discuss suspending Syria’s membership. (Foto:AP/dapd)
Hoto: AP

Shugabannin kungiyar hada kan kasashen Musulmi na OIC za su gana a birnin alQahira na kasar Masar domin neman hanyar warware yakin basasar kasar Siriya da kuma yakin da Faransa ke jagoranta a kasar Mali da nufin dakile matsalar masu kishin addinin da suka mamaye yankin arewacin kasar a watanni baya, bayan daukar matakin soji akansu. A wannan Litinin ne ministocin kula da harkokin wajen kasashen kungiyar su 57 ke fara gudanar da taron yini biyu domin share fagen taron shugabannin kungiyar, wanda zai sami halartar shugabannin kasashe 26. A lokacin taron ne dai shugaban kasar Masar Mohamed Morsi, zai karbi ragamar jagorancin karba-karba na kungiyar.

A cewar babban sakataren kungiyar, Ekmeleddin Ihsanoglu dama tun a shekara ta 2011 ne ya kamata a gudanar da babban taron kungiyar kasashe Musulmin, amma aka jinkirta yinsa sakamakon guguwar sauyin da take kadawa a kasashen Larabawa, wadda ta yi awon gaba da wasu shugabannin kasashen, ciki harda shugaban Masar Hosni Mubarak. Sakataren , wanda tsohon jami'in diflomasiyya ne daga kasar Turkiyya ya ce babban taron, zai baiwa kasashen da ke cikin kungiyar damar daidaita manufofin su na ketare dangane da rikice-rikicen da ke faruwa domin daukar matakin daya dace wajen warware su.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe