SiyasaAfirka
Nazarin dangantakar EU da kasar Nijar
September 25, 2023Talla
Dan majalisar na jam'iyyar Social Democratic SPD Christoph Schmidt, ya shaida wa DW cewa akwai bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta san huruminta a yankin Sahel da kuma yin tunani mai zurfi kafin daukar matakin sake kulla alaka da Nijar ba tare da kasar Faransa ba.
Schmidt ya ce abin da ya kamata a sanya a gaba shi ne ci gaba da tattaunawa da sojojin da ke mulkin kasar, kamar yadda kasar Amurka ta kudiri aniyar yi, duk da cewa Macron na da hujja cewa har yanzu Bazoum ne halastaccen shugaban kasar don bai yi murabus ba.