1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 25 na bikin tuna kisan Yahudawa

January 27, 2021

A ranar 27 ga watan Janairu na kowacce shekara, ake gudanar da bikin tunawa da kisan kare dangi da gwamnatin 'yan Nazi a Jamus ta yi wa Yahudawa.

Deutschland Holocaust Gedenktag Bundestag Berlin
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Rabbi Shaul NekrichHoto: Odd Andersen/REUTERS

Tun daga shekara ta 1996, ake gayyatar wadanda suka tsira daga kisan kiyashin da gwamanatin 'yan Nazi ta yi wa Yahudawa da gwamnatocin kasa da kasa domin gabatar da jawabi a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, a ranar 27 ga watan Janairu na kowacce shekara, domin tunawa da wadanda aka yi wa kisan kiyashin. A wannan shekarar ne dai ake cika shekaru 25 da wannan kisan kiyashin, inda a rana 27 ga watan Janairun shekara ta 1945, sojojin Tarayyar Soviet suka rusa sansanin gwale-gwale na 'yan Nazi da ke Auschwitz a Jamus din.

Karin Bayani: Manyan wakilan Musulmi da Yahudawa a Auschwitz

A irin ranar ne ma a shekarar 1998, wato shekaru 53 bayan rufe sansanin na Auschwitz, masanin tarihin Isra'ila Yehuda Bauer ya gabatar da jawabi ga majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, inda ya bankado wani kisan kiyashi da ya faru a Ruwanda a shekarar 1994 da kuma Kambodiya a 1975 zuwa 79 sai kuma wanda aka yi a Armeniya a shekara ta 1915 zuwa 1916.

Dandalin tunawa da Yahudawa a BerlinHoto: Markus Schreiber/AP Photo/picture alliance

Bayanan nasa dai sun sauya fasalin yadda ake ganin kisan kiyashi a karni na 20. Amma Bauer ya ce kisan da aka yi wa Yahudawa na musamman ne, ya kuma yi gargadin za a kuma yi amma ta wata siga dabam mai yiwuwa makamanciyar wanda aka yi a baya. To sai dai yunkurin goge bakin fentin Jamusawa kan kisan kiyashin abu ne mai matukar wahala, kamar yadda tsohon shugaban Jamus din Roman Herzog ya fada loakcin kaddamar da ranar tunawa da kisan. 

Karin Bayani:Shekaru 75 da kawo karshen sansanin Nazi a Auschwitz

A shekara ta 2002, lokacin da tsohon ministan harkokin wajen Poland Bronislaw Gremek daya daga cikin wadanda suka tsira daga kisan kiyashin ya yi magana a bikin tunawa da kisan Yahudawan, duniya ta mayar da tunaninta kan harin ranar 11 ga watan Satumba da aka kai Amirka. Kowace shekara har zuwa 2007, wadanda suka tsira daga kisan kiyashin, na yin jawabi a ranar tunawa da kisan kiyashin da 'yan Nazin suka yi.

Manyan wakilan Musulmai da na Yahudawa sun kai ziyarar hadin gwiwa a Auschwitz

02:43

This browser does not support the video element.

A shekara ta 2010, Shimon Peres shi ne shugaban Isra'ila na farko da ya fara gabatar da jaje a wani gidan tarihin Reichtag da ke birnin Berlin, inda ya yi gargadi ga masu yi wa Isra'ilan barazana da makaman kare dangi, babu shakka yana shagube ne ga kasar Iran. Ya kara da cewa ya rage garemu mu koyawa 'ya uwanmu mutunta rayuwar dan Adam tare da tabbatar da zaman lafiya tsakanin kasahen duniya. Peres ya karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekara ta 1994 tare da tsohon Firaministan Isra'ila Yitzchak Rabin da kuma shugaban Falasdinawa Yasseer Arafat.

Karin Bayani: Musulmai a sansanin gwale-gwale

Tun bayan da daruruwan 'yan gudun hijira da suka tsarewa yakin basasa daga Afirka da Asiya suka fara yada zango a Turai, batun ya zama abin magana a ranakun tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa yahudawa, a cewar Ruth Küger, wacce ta sha da kyar daga kisan kiyashin a Ostiraliya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani