1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mandela: Gwarzo ya cika shekaru 100

Binta Aliyu Zurmi MNA LMJ
July 18, 2018

A ranar 18 ga watan Yuli ake bikin cika shekaru 100 da haihuwar Nelson Mandela. Mandela ya shahara a dalilin gwagwarmayar da ya yi ta samar da daidaito da kawar da wariyar launin fata a kasarsa ta Afirka ta Kudu.

Nelson Mandela mit Cyril Ramaphosa
Mandela da Cyril Ramaphosa shugaban Afirka ta Kudu me ciHoto: picture-alliance/AP Images/J. Parkin

An haifi Mandela a ranar 18 ga watan Yulin shekara ta 1918. Mahaifinsa mai suna Gadla ya rada masa suna Rolihlahla wato‚ dan gwagwarmaya a harshen su na Xhosa, al'amarin da ba zai rasa nasaba da akidar Mandela ta kawo canji ba tun lokacin kuruciya.

Mandela ya shiga jam'iyyar ANC a shekara ta 1944 lokacin yana shekarun samartaka kuma shekaru hudu kafin kafuwar jam'iyyar National Party wacce ta assasa yaki da kyamar launin fata a Afirka ta Kudu kamar yadda marigayi Mandela ke yawan fadi:

"Na yi yaki da mulkin danniya na Turawa kuma ba yaki mulkin danniya na bakar fata kadai ba, burina shi ne shimfida dimukuradiyya a kasa yadda kowa zai zama daidai da kowa ba tare da bambanci ba."

Mandela sananne a AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/U. Deck

Da yake karin haske a kan marigayi Mandela sanannen dan jarida a kasar Zimbabuwe Mlondolozi Ndlovu ya yi karin haske kamar haka:

"A matsayinsa na shugaban kasar Afirka ta Kudu baki na farko wanda ya yi Allah wadai da cin zarfin fararen da ke kasar wadanda kuma sune marasa yawa a kasar. Dan kasa nagari mai dagewa a kan manufofinsa."

Mandela ya shafe dogon lokaci a gidan kaso, inda daga baya aka sake shi amma aka ba shi zabin barin kungiyarsu wanda hakan ya sa ya ce ba ya so, gwamma ya ci gaba da zamanshi. Irin wannan jarumtaka da ma jajurcewa na Mandela ya sa mutane da dama ke sha'awarsa kamar David Noah dan asalin kasar Gambiya wanda ke karatun aikin jarida.

Mandela ya kasance abin tunawa tsakanin 'yan fafutikaHoto: picture-alliance/dpa

Mandela ya ci gaba da fafutukar kawar da wariyar launin fata. A watan Afrilu na 1994 kasar Afirka ta Kudu ta yi zaben gama gari inda ya zamo shugaban kasa bakar fata na farko. Rashin cin nasarar kawar da talauci da wariyar launin fata baki daya a kasar ya sa wasu ke ganin gazawarsa.

Rashin son kanshi da kokarin da ya yi na kawo daidaito a cikin al'umma na daya daga cikin muhimmman abubuwan alfaharinsa. Daga karshen rayuwar Mandela ya yi murabus daga duk wata fafutika don samun lokaci na iyalensa. A ranar biyar ga watan Disamba 2013 Allah Ya dauki rayuwar Mandela, inda duniya gaba daya ta yi jimamin mutuwarsa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani