1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman a bincike take yancin ɗan Adam a Masar

Usman ShehuAugust 20, 2013

Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na neman sai hukumomin Masar su bar jami'an ƙasashen waje, su gudanar da binciken cin zafarin jama'a

Security forces in Alexandria take safety measures in case of an anti-coup demonstration out front of the El-Kaid Ibrahim mosque. Ibrahim Ramadan - Anadolu Agency Keine Weitergabe an Drittverwerter.
Sojoji da masu zanga-zanga a MasatrHoto: picture-alliance/AA

Hukumar kula da kare yancin ɗan Adama ta MDD ta buƙaci hukumomi a ƙasar Masar da su bar jami'an ƙasa da ƙasa su shiga ƙasar, don gudanar da bincike bisa take yacin jama'a, yayin tarwaza masu adawa da juyin mulkin soji, wanda hukumomi a ƙasar ta Masar suka yi a makon jiya. Kakakin hukumar Liz Trossell, na mai cewa suna matsawa hukumomin Masar lamba da su bar tawagar kula da kare yancin ɗan Adam da ta ziyarci ƙasar. Tun dai a makon jiya shugaban humar Navi Pillay ta buƙaci da a bar masu bincike daga ƙasa da ƙasa, masu zaman kansu da su gudanar da bikicike kan yadda aka yi amfani da ƙarfi a rikicin na Masar.

A gefe guda shi ma Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi mummunar suka bisa yadda sojojin na Masar suka tinkari siyasar ƙasar. Ban ki-moon yace a kaɗu da mutuwar 'yan Muslim Brotherhood 37 yayinda suke tsare a hannun jami'an tsaro. Kana ya soki kisan da aka yi wa 'yan sanda 25 a yankin Sinai.

A wani labarin da ya shafi rikicin siyasa: Hukumomi a ƙasar Masar sun tsare Mohamed Badie, jagoran addini na ƙungiyar Muslim Brotherhood, bisa tuhumar sa da hannu wajen kisan masu zanga-zanga a watan Juni.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu