1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mafita ga 'yan adawa na Kamaru

Zakari Sadou
September 29, 2025

Gabanin zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, da alama haɗakar ɓangaren adawar ƙasar na ci gaba da samun ƙarin gwiwa, a koƙarin su na kawar da gwamnatin shugban ƙasar Paul Biya wanda ya shafe fiye da shekaru 40 kan madafun iko.

Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru
Shugaba Paul Biya na kasar KamaruHoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

 

Bayan da Ateki Seta Caxton ya janye takararsa tare da bayyana goyon baya ga dan takarar jam'iyyar UNDP Bello Bouba Maigari tsohon hannun damar shugaba Biya, wanda kuma ya fito daga yankin Arewa mai ƙuri'u masu yawa, wannan karon kuwa Akere Tabeng Muna Fitaccen lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam ne shima ya janye takararsa na goyon bayan Bello Bouba Maigari wanda ake ganin yana cikin manyan ƴan adawa a zaɓen.

Tarnakin da ake fuskanta

Bello Bouba Maïgari dan adawa a zaben KamaruHoto: Henri Fotso/DW

Ba dai wannan ne karon farko da Muna ya janye daga takarar shugaban kasa a Kamaru ba, domin ko a 2018 ya janye domin mara wa jagoran ƴan adawar ƙasar, Maurice Kamto baya

Bello Bouba Maigari dan takarar zaben shugaban kasa ya ce yanzu ba lokaci bane na kyawawan jawabai, da kuma daukan alkwarin da ba za a iya cikasu ba.

Neman mafita

Sai dai duk da ƙawancen da aka ƙulla tsakanin Bello Bouba Maigari da Akere Muna da kuma Ateki Caxton, ministan yankuna, Paul Atanga Nji ya ce an riga a wuce lokacin da hukumar zaɓe za ta iya amincewa da duk wata haɗakar jam'iyyu.

Issa Bakary Tchiroma dan adawa a zaben KamaruHoto: picture-alliance/dpa/MAXPPP/ J.-P. Kepseu

Ya yi zargin cewa akwai wasu ƴan takara masu neman tayar da zaune tsaye ta hanyar kawo cikas ga tsarin zaɓen da gudanar da zanga zanga da kuma yaɗa sakamakon ƙarya.

Sai dai ministan yayin taron manama labalai, bai bayyana sunayen yan takara da aka samu da laifin ba, ya ce za a dauki hukunci mai karfi kan wadanda aka samu da laifin.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani