1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro a yankin Sahel

November 8, 2021

Matasan kasa da kasa sun gudanar da taron kwanaki uku a kokarinsu na neman mafita game da batun matsalolin tsaro da kuma bakin haure.

Agadez Nigeria Flüchtlingslager
Hoto: Getty Images/AFP

A  birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar kungiyar Alternative Espace Citoyen ce ta gudanar da taron yini uku game da batun matsalar bakin haure da kuma tabarbarewar tsaro.

Taron da ke zaman na kasa da kasa ya samu halartar matasa kimanin 400 da suka fito daga yankunan

Matasa 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/dpa/J. Delay

jihohi daban daban da kuma wasu kasashen ketare irin su Mali da kuma Senegal a kokarin su na neman mafita daga matsalolin zuwa ci rani ko bakin haure da kuma tabarbarewar tsaro.

OXFAM ce dai ta tallafa da kudaden gudanar da taron da ke zaman na shekara shekara da yan farar hular na Alternative suka saba gudanarwa a kasar da ke yankin Sahel da

tabarbarewar tsaro gami da safarar bakin haure ke kara daukan wanisabon salo.

Taron matasan da ke zaman na akwai a tarihi, tabbas ya samu halartar takwarorin matasan kasar kuma  'yan fafutuka daga kasashen ketare, bayan wasu daruruwa ko dubbai da ke bibiyar sa a kai tsaye ta yanar gizo daga kusurwoyi daban daban na kasashen duniya.

Cibiyar 'yan gudun hijira a AgadezHoto: Imago Images

Duba da yadda  matasan ke cewar lokaci yayi kuma manda ya ishi kan kaza game da matsalolin tsaro a kasashen yankin Sahel da kuma batun ci rani da kungiyoyin fafutuka  ke zargin magabata da tauye hakkin dan Adam.

A daura da taron matasan dai su ma magadan gari sun gudanar da makamancin wanan taro game da siyasar Nijar bisan kan ci rani.