1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bukaci sasanta rikicin Togo

Gazali Abdou Tasawa
September 18, 2017

Kungiyar limaman Kristoci mabiya darikar Katolika ta kasar Togo ta yi kira ga bangarorin siyasar kasar da su mutunta tanade-tanaden da kundin tarin mulkin kasar na shekara ta 1992.

Togo Protest #Faure Must Go
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Kungiyar limaman Kristoci mabiya darikar Katolika ta kasar Togo ta yi kira ga bangarorin siyasar kasar da su mutunta tanade-tanaden da kundin tarin mulkin kasar na shekara ta 1992 ya yi a game da wa'adin mulkin shugaban kasa da ma tsarin gudanar da zabe. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da majalisar dokoki ke gudanar da muhawara kan batun yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima da nufin shawo kan rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.

A cikin wata sanarwa da suka fitar da kuma aka karanto a illahirin coci-coci na kasar a ranar Lahadi, Limaman Kiristocin mabiya darikar Katolika, sun bayyana damuwarsu dangane da rikicin siyasar da kasar ta shiga inda suka yi kira ga bangarorin siyasar kasar kan su kai zuciya nesa su kuma nemi hanyoyoin sulhu wajen shawo kan rikicin.

Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Amma kuma sun yi kira ga gwamnatin kasar wacce yanzu haka ta shigar da wasu kudirorin doka na yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara fuska a gaban majalisar dokoki da ta kiyaye da ma mutunta tanade -tanaden da kundin tsarin mulkin kasar na shekara ta 1992 ya yi a game da abun da ya shafi kayyade wa'adin mulki da kuma tsarin shirya zabe. Monseigneur Denis Amouzou Djakpa shi ne Akbishop na babbar cocin birnin Lome na daga cikin limaman Kiristocin da suka yi wannan kira a lokacin zaman cocin na karshen mako.

Babban Akbishop din na birnin Lome ya jaddada bukatar ganin gwamnati ta nuna kyakyawar aniya da kuma dattaku a cikin lamarin ta yadda za su nunawa 'yan kasar ta Togo cewa da gaske suke suna son ganin an kawo karshen wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa shekaru da dama.

Hoto: picture alliance/AA/ Alphonse Ken Logo

Shugabannin Kiristocin sun kuma bayyana damuwarsu da yadda jami'an tsaro ke muzgunawa jama'a a wasu garuruwa na kasar. A kan haka ne suka yi kira ga sojojin kasar da su kasance 'yan baruwanmu a cikin rikicin siyasar kasar kamar adda kundin tsarin mulkin kasar ta Togo ya umurce su. Kazalika sun yi kira ga shugabannin siyasa na kasar na bangaran masu mulki da na Adawa da su kauce wa shirya zabukan gangami a rana daya wadanda ka iya rikidewa zuwa fada tsakanin bangarorin biyu da kuma ka iya haddasa asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Yanzu dai mutanen Togo sun kashe kunne suna sauraran sakamakon da muhawarar da majalisar dokokin kasar take yi kan batun neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima za ta haifar. Sabuwar dokar da gwamnatin ta gabatar a gaban majalisar ta tanadi kayyade wa'adin mulkin Shugaban kasa zuwa wa'adi biyu, sai dai kuma ba za ta waiwaye abin da ya wuce ba, wanda ke nufin Shugaba Faure Gnassingbe wanda ke kan karagar mulkin kasar tun a shekara ta 2005 na iya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa, batun da 'yan adawa ke cewa ba za ta sabu ba.