Neman Taimakon gaggawa a Pakistan
August 13, 2010Gwamnatin ƙasar Pakistan ta musanta zargin da ake mata na hana 'yan jaridu gabatar da rahotannin da suka shafi matsalar anbaliyar ruwan dake ci gaba da haddasa hasarar rayuka dana dukiyoyi a ƙasar.
Yanzu haka dai hukumomin bada agajin gaggawa a Pakistan sun bayyana fargaban ɓarkewar cutuka a yankunan da anbaliyar ruwan ƙasar yayiwa ɓarna. Kawo yanzu dai kimanin mutane miliyan 14 ne anbaliyar ruwan ya tagayyara, a yayin da wasu 1600 suka rasa rayukansu. Majalisar ɗinkin duniya tace tana fargaban ɓarkewar cutuka masu yaɗuwa da suka haɗa da cutar kwalara da amai da gudawa da kuma zazzaɓin cizon sauro.
Tuni dai majalisar ɗinkin duniya ta ƙaddamar da asusun neman taimako na euro miliyan 350 domin samar da abinci da matsugunai da kuma magunguna. Jakadan Pakistan a majalisar ɗinkin duniya Abdullah Hussain Haroon ya baiyana buƙatar ƙasashen duniya su farga tare da kai agaji cikin gaggawa. Tuni dai wasu ƙasashen na duniya sukayi alƙawarin bada gudumawar euro miliyan120, inda jamus ta bada euro miliyan 10.
A wani lokaci a yau ne Babban magatakardar majalisar ɗinkin duniya Ban ki-moon ya shirya kai ziyara a yankin da anbaliyar ruwan yayiwa ɓarna.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Zainab Mohammed Abubakar