Netantahu ya kammala ziyarar da ya kai a Afirka
July 7, 2016A karshen ziyarar tashi A wannan Alhamis din, Netanyahu ya yi jawabi a gaban 'yan majalisun dokokin kasar ta Habasha inda ya ce, muna masu gani a zahiri irin mahimman abubuwa masu babban amfani da kasar Habasha da ma Afirka suka kumsa, kuma yana mai cike da farin cikin sanar musu cewa Isra'ila na da babban buri ga kasashen Afirka a fannoni da dama.
Wannan ziyara dai ta wani shugaban gwamnatin Isra'ila da ke zaman irinta ta farko a kasashen na Afirka da ke Kudu da Sahara, ta zamanto wani abun tarihi a cewar Firaministan na Isra'ila. A shekara ta 1960 ne dai kasashen Afirka da dama suka soma raba gari da Isra'ila sakamakon yakin da ta yi da makwabtanta Larabawa tsakanin 1967 zuwa 1973, sannan ga batun huldar kasar ta Isra'ila da gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.