1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Netanyahu na fuskantar matsin lamba daga masu zanga-zanga

May 13, 2024

A yayin da Isra'ila ke shirin gudanar da bikin ranar samun 'yancin kai, masu zanga-zanga na kara matsa lamba don sako fursunonin yaki da Hamas ke rike da su a Gaza.

Hotunan masu zanga-zanga da ke neman a sako mutane da Hamas ta kama
Hotunan masu zanga-zanga da ke neman a sako mutane da Hamas ta kamaHoto: Tania Kraemer/DW

Masu zanga-zanga na ganin gwamnatin Netanyahu ta gaza wajen kubuto da mutane da Hamas ta kama tun harin bakwai ga watan Oktoba.

Tattaunawar da ake yi don sako fursunonin bata samu nasara ba a yayin da Isra'ila ta fara ruwan wuta kan Rafah.

Karuwar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami'o'in Amurka

An nuno daya daga cikin masu zanga-zangar Amos Cividalli dauke da wani allo mai lamba 218 da ke nuna adadin kwanaki da 'yan Isra'ila 128 suka shafe a hannun Hamas.

 

Daya daga masu zanga- zangar ya ce bai aminta da gwamnati ba kuma yana ganin ta gaza wajen ceto 'yan kasar da ke hannun Hamas.

 

Dubban 'yan Isra'ila na zanga-zangar adawa da gwamnati