Yakin Gaza: Netanyahu na fuskantar matsin lamba
June 5, 2024Firanmintan Isra'ila Benjamin Netanyahu na fuskantar matsin lamba daga bangarori daban-daban kan matsayarsa game da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yakin Gaza da shugaban Amirka Joe Biden ya gabatar. Shugaba Biden ya gabatar da sabon daftarin yarjejeniya da ma tsarin yadda za a saki wadanda ake tsare da su. Sai dai kuma Mista Netanyahu ya yi watsi da bukatar.
Karin bayani:Gaza: Amurka ta gabatar da sabon shirin tsagaita wuta
Majalisar ministocinsa dai sun yi barazanar yin murabus idan har ya amince da yarjejeniyar gabanin Isra'ilar ta ci galaba a kan kungiyar Hamas, yayin da jagoran gudanarwa da ke sa ido kan yakin da kasar ke yi, Benny Gantz shi ma yayi barazanar aje mukaminsa idan Netanyahu ya ki amincewa da yarjejeniyar.
Karin bayani: Isra'ila: Netanyahu na fuskantar bore daga majalisar yaki
Ko a ranar Talata, kasar Qatar da ke shiga tsakani a yakin Gaza ta ce tana dakon matsayar da Isra'ila za ta dauka kan yarjejeniyar da har yanzu babu wata kwakwarar matsaya daga bangarorin biyu da ke fada.
Har wayau, Shugaba Biden ya zargi Netanhayu da jan kafa ga yayyafa ruwa ga rikicin domin cimma wata manufarsa ta siyasa.