1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya goyi bayan 'yan kasar Iran da ke zanga-zanga

January 5, 2026

Yayin da al'umar kasar Iran ke gudanar da zanga-zangar adawa da tabarbarewar tattalin arziki, Isra'ila ta goyi bayan boren. Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce 'yan Iran na iya daukar makomarsu da kansu.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanjahu yana jawabi a birnin Kudus
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanjahu yana jawabi a birnin KudusHoto: Ronen Zvulun/UPI Photo/IMAGO

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana goyon bayansa ga al'ummar Iran, yana mai cewa duniya na iya ganin manyan sauye-sauye a kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a farkon taron majalisar ministoci a birnin Kudus, inda ya ce Isra'ila na tare da burin ‘yan Iran na samun ‘yanci da adalci da ma dimukuradiyya.

Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da matsin tattalin arziki a Iran din.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya kuma ce akwai yiyuwar ‘yan Iran su dauki makomarsu a hannunsu.

A shekarar da ta gabata, Isra'lar ta yi arangama da Iran na tsawon kwanaki 12, tare da kai hare-hare kan wasu muhimman wuraren nukiliya, tana zargin Tehran da shirin kera makaman nukiliya.