Netanyahu ya samu koma baya a zaben Isra'ila
January 23, 2013A zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar ranar Talata a Isra'ila jam'iyar 'yan ra'ayin rikau ta Firaminista Benjamin Netanyahu ta samu koma baya. Bisa alkalumman da hukuma ta bayar jam'iyarsa ta Likud-Beitenu ta samu yawan kujeru 31 daga cikin 120 na majalisar dokoki ta Knesset. Hakan na nufin kenan kawancen jam'iyar Netanyahu ta yi asarar kujeru 11 a majalisa. Jam'iyar da ta samu ci-gaba a zaben na ranar Talata ita ce jam'iyar Yesh Atid ta masu sassaucin ra'ayi dake karkashin jagorancin tsohon dan jarida Jair Lapid, wadda ta tashi kujeru 19 wato kenan ita zo ta biyu. A matsayin shugaban jam'iyar da ta fi yawan kujeru, Netanyahu zai yi kokarin kafa kawance.Tun da farko Jair Lapid ya nuna cewa zai shiga kawance da Netanyahu bisa wasu sharudda.
"Zai yi muni ga Isra'ila idan muka samu wata gwamnati da ta kunshi ''yan ra'ayin rikau da masu kaifin kishin Yahudanci. Muna bukatar wani kawance da dukkan jam'iyun Isra'ila ke da wakilici a cikinsa."
Netanyahu dai ya ce babban nauyin dake kan sabuwar gwamnati shi ne yaki da matakan Iran na mallakar makaman nukiliya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman