1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya sauka a Amurka

July 28, 2026

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya isa birnin Washington domin ganawa da shugaban Amurka Donald Trump, inda ake sa ran za su tattauna rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman yakin da suke yi da Iran.

Benjamin Netanyahu da Donald Trump a ranar 29.12.2025
Benjamin Netanyahu da Donald Trump a ranar 29.12.2025Hoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Netanyahu ya ce babban burinsa shi ne tabbatar da tsaron Isra'ila da kuma fadada zaman lafiya a yankin. Ya bayyana hakan ne kafin ya bar Isra'ila zuwa Amurka.

Wannan shi ne karon farko da shugaban na Isra'ila ke ziyartar Amurka tun bayan ziyararsa ta karshen watan Fabrairun wannan shekara, kafin rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Iran tare da shiga tsakani da Amurka.


Karin bayani: Trump ya tattauna da Netanyahu kan yankin Gulf

Ziyarar na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa Trump na nuna rashin gamsuwa da yadda Netanyahu ke tafiyar da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, duk da ci gaba da hadin gwiwa kan batutuwan tsaro da kasashen biyu ke yi.