Netanyahu ya yi barazanar lalata Lebanon saboda Hezbollah
October 8, 2024Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga 'yan Lebanon da su ceto kasarsu daga hannun kungiyar Hezbollah, ko kuma sun fuskanci farmakin da zai haifar da wahala kamar yadda ya wakana a Gaza. A cikin wani sakon bidiyo da aka watsa cikin harshen Ingilishi, Netanyahu ya yi barazanar ganin bayan shugabannin Hezbollah, inda ya ce dakarunsa sun kawar Hassan Nasrallah tsohon shugaban Hezbollah da wanda ya maye gurbin Nasrallah da jagoran baya-bayannan nan da aka zaba, amma ba tare da bayyana sunansa ba.
Karin bayani: Tuni da ranar harin ba-zata a Isra'ila
Isra'ila ta kai wasu hare-hare ta sama a kudanci da gabashin Lebanon, da kuma kudancin birnin Beirut da ke zama tungar 'yan Hezbollah. Sai dai kungiyar ta dauki alhakin kai hare-haren rokoki kan cibiyoyin soji a birnin Haifa da ke arewacin Isra'ila, inda aka harba makamai kusan 85. Har ila yau Hezbollah ta yi ikirarin fatattakar sojojin Isra'ila da ke kutsawa kudancin Lebanon musamman ma a kusa da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.