1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tuhumi Netanyahu da cin hanci da rashawa

Binta Aliyu Zurmi
January 28, 2020

Wata kotu a Isra'ila a hukumance ta tuhumi Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da laifukan cin hanci da rashawa da kuma amfani da mukaminsa wajen yiwa wasu alfarma.

Israel Benjamin Netanjahu in der Knesset
Hoto: Getty Images/AFP/G. Tibbon

Tuhumar na zuwa ne jim kadan bayan da Firaiministan ya janye bukatar da ya gabatar wa majalisar dokokin kasar ta neman rigar kariya.

Wannan ba shine karon farko da ake tuhumar Benjamin Netanyahu wanda ya shafe shekaru 13 yana jan ragamar mulkin Israila da laifin cin hanci da rashawa ba, zargin da ya sha musantawa a baya da cewa bita da kullin siyasa ne kawai.

A nan gaba ne kotu za ta sanar da ranar zai gurfana a gabanta.