1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

New York na fuskantar karin yawan masu fama da Corona

Mohammad Nasiru Awal MAB
March 25, 2020

A birnin New York da ke da cunkoson gidaje da kuma yawan al'umma fiye da miliyan takwas, jami'an kiwon lafiya ke kokarin samun gadajen asibiti ga majinyata cutar Corona.

USA New York Citiy | Coronavirus
Hoto: Reuters/A. Kelly

Jihar New York na kasar Amirka ta sake shiga mawuyacin hali na yawaitar masu kamuwa da cutar Covid-19, abin da ya jefa asibitoci a jihar da ke zama cibiyar annobar Coronavirus a Amirka cikin kakanikayi. Hakan na zuwa ne yayin da jihar California ta ce tana iya zama jiha ta gaba da za ta fuskanci karin yaduwar cutar.

A birnin New York da ke da cunkoson gidaje da kuma yawan al'umma fiye da miliyan takwas, jami'an kiwon lafiya ke kokarin samun gadajen asibiti ga majinyata cutar Corona yayin da yawan wadnada suka rasu sakamakon cutar ya kai mutum 210 a jihar, sannan an tabbatar da mutum dubu 25 da 600 sun kamu da Covid-19. Ana bukatar gadajen asibiti dubu 140 a New York, abin da ya ninka kusan sau uku yawan wadanda ake da su.

Fadar White House ta shawarci duk wanda ya ziyarci New York ko ya bar birnin da ya killace kanshi tsawon kwanaki 14, don hana yaduwar cutar.