SiyasaTurai
New Zealand ta yanke wa dan ta'adda hukunci
August 27, 2020Talla
Alkalin babbar kotun Christchurch Cameron Mander ya shaida wa dan bindigar cewa koda ya share rayuwarsa gabadaya a gidan yari ba zai biya irin barna da mugun hali da ya nuna wa wadanda ya hallaka ba.
Firaministar New Zealand Jacinda Ardern wace tun farko ta yi Alla-wadai da harin da ya faru a shekarar da ta gabata, ta ce ta yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke a safiyar Alhamis din nan.