1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta yi tir da juyin mulki a Guinea Conakry

Uwais Abubakar Idris
September 6, 2021

Bacin rai da da Allah wadai ne suka biyo bayan hambarar da gwamnatin dimukurdiyya ta kasar Guinea Conakry da sojoji suka yi a yanayin da ke nuna koma baya ga mulkin dimukurdiyya a wannan kasa ta yammacin Afrika

Sojoji karkashin jagorancin Mamady Doumbouya da suka yi juyin mulki a Guinea Conakry
Sojoji karkashin jagorancin Mamady Doumbouya da suka yi juyin mulki a Guinea ConakryHoto: Radio Television Guineenne/AP Photo/picture alliance

 

Najeriya kasance kan gaba wajen maida martani a kan abinda ya faru a Guinea Conakry inda ma’aikatar kula da harkokin kasashen wajen kasar ta fitar da sanarwa inda ta bayyana cewa ba za ta amince sojoji su kifar da zababbiyar gwamnatin dimukurdiyya ba. Esther Sunsuwa ita ce jami’ar yada labaru ta ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriyar.

Jama'a a Guinea Conakry na jinjina ga sojoji da suka yi juyin mulkiHoto: Souleymane Camara/REUTERS

‘’Najeriya ta yi bakin ciki da juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Guinea domin wannan ya sabawa kudurin kungiyar Ecowas a kan zababbiyar gwamnati, shi yasa Najeriya ta yi Allah wadai da shi, duk wani sauyi na gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba Najeriya ta yi Allah wadai da shi, don haka Najeriya na kira a maido da gwamnatin dimukurdiyya a kasar."

Kasar Guniea dai ta dade tana fuskantar rigingimu na siyasa tun lokacin da hambararen shugaban kasar Alpha Conde mai shekaru 83 ya fara wa’adi na uku na mulkinsa bayan da ya sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaban sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar ta Guinea Lietenant Col Mamady Dounboya yace almubazaranci da dukiyar kasa ya sanya suka kifar da gwamnatin, wacce al'ummarta ke cikin mawuyacin hali. Gilbert Temba wani dan kasar Guniea Conakry ne da ke Abuja ya baiyana yadda ya ji da juyin mulkin?

Shugaban kasar Ghana kuma shugaban kungiyar ECOWAS Nana Akufo-AddoHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

’Yace babu shakka a matsayina na dan kasar Guinea wannan mummunan abu ne ga dimukurdiyyarmu, ba wanda zai yi murna in ya ji labarin juyin mulki a kasarsa, wanda zai maida mu baya ya kara wahalhalu ga jama’a. Dama al’amura sun shiga cikin wahala tun lokacin da hambararen shugaban kasa ya zarce zuwa wa’adi na uku’’

Ita ma kungiyar Ecowas ta ce juyin mulkin ya sabawa kaidoji da kudurorinta, ta bukaci sojojin su sako shugaba Conde da suka kama kuma su maido da dimukurdiyya. Sanin cewa sannu a hankali ana ganin karuwar sojoji na kifara da gwamnati a yankin Afrika ta yamma, domin ya faru a Mali yanzu kuma ga Guinea.

Guinea Conakry dai ‘yar karamar kasa ce mai yawan al'umma milyan 13, wacce duk da arzikin ma’adanai da Allah ya hore mata take fama da talauci.