1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Alamun haramtar takara ga Hamma Amadou

Salissou Boukari
April 11, 2018

Kotun karya shari'o'i ta Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da karan da madugun 'yan adawar kasar Hama Amadou ya shigar a gabanta, bayan yanke masa hukuncin dauri na shekara daya da wata kotun tayi.

Hama Amadou
Hoto: DW/S. Boukari

Hama Amadou dai na fuskantar shari'a tun da dadewa dangane da batun mallakar jarirai da ba nasu ba, da ake zarginsa shi da mai dakinsa. Yayin da muka tumtubi Masanin kundin tsarin mulki a kasar ta Nijar Amadou Boubakar Hassan wanda ya ce korar karan da wannan kotu ta yi na nufin cewa duk lokacin da Hama Amadu ya shigo kasar ta Nijar sai ya yi wannan kaso da aka yanke masa.

Masanin kuma ya kara da cewa ga yadda kundin zaben kasar ta Nijar ya tanada, idan har ba a yafewa Hama Amadou wannan laifi ba, to ba zai samu incin yin zabe ko kuma na tsayawa takara ba.

Tsohon Firaminista, kuma tsohon shugaban majalisar dokoki, wanda ya zo na biyu a zagaye na farko na zaben shugaban kasar da aka yi a Nijar na 2016 an yanke wa Hama Amadou hukuncin dauri na shekara daya a gidan kaso ba tare da yana cikin kasar ba, wanda tuni wasu daga cikin wadanda ake zargin sama da 20 cikinsu kuwa har da mai dakin ta hama Amadou suka kammala wa'adin zamansu na gidan kaso.