1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: an samu karuwar yan gudun hijira

May 18, 2021

Ofishin gudanar da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ya ce cikin kwanaki uku an samu kwararr yan gudun hijira.

Mosambik | Provinz Cabo Delgado | Vertriebene Kinder Opfer von Terrorismus
Hoto: Roberto Paquete/DW

Kimanin mutane sama da dubu 1goma ne su ka yi gudun hijira daga yankin yammacin kasar sakamakon hare-haren yan bindiga.

Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutanen sun yo hijira ne daga yankin Anzourou ya zuwa birnin Tillaberi yayin da wasu kuma ke danganawa da Yamai fadar gwamnatin ta Nijar domin tsira da rayukansu.

Kawo yanzu dunbin mutane da ba a tantance yawansu ba daga yankin da abin ya yi kamari, na cigaba da kwarara a wasu manyan garuruwa inji masu bayar da agajin. A wannan watan kadai kimanin mutane sama da ashirin ne yan ta'adda suka aika lahira, baya ga wasu goma sha uku da suka hallaka a watan da ya gabata.