Nijar: Ana dakon gwamnatin hadin kan kasa
August 30, 2016A kwanakin da suka gabata ne dai wasu jam'iyyun adawa musamman ma dai jama'iyyar MNSD Nasara suka amince da su shiga gwamnati da nufin girka gwamnatin hadin kasa a Nijar din. Tun bayan wannan lokaci ne da al'ummar kasar ke zuba idanu don ganin irin gyaran fuskar da shugaban kasar zai yi wa gwamnatinsa da ya riga ya girka bayan da aka rantsar da shi a wani sabon wa'adin mulki.
Su ma dai 'yan siyasar da suka amince su shiga gwamnati na ta zuba idon ganin irin mukaman da za su samu a gwamnatin hadin kasa, su kuma 'yan kugiyoyin fararen hula na kasar cewa suke wannan yanayi da aka shi ya sanya komai a kasar ya tsaya cik sabanin yadda lamura suke tafiya a kwanaki ko makonnin da suka gaba gabannin fara wannan magana ta kafa gwamnatin hadin kasa.
Su kuwa wasu 'yan kasar kamar Nasiru Saidu cewa suka yi kafa gwamnatin ne ya dame su ba, irin yawan ministocin da kasar za ta kunsa bayan an kafa gwamnatin hadin kan kasar ne abin dubawa. Baya ga haka wani abu da wasu ke dubawa shi ne irin mutanen da za a nada kan mukamai domin a cewar wasu 'yan kasar kyautuwa ya yi a zabo mutane masu nagarta don danka musu amana ta jagorantar ma'aikatu da hukumomin gwamnati.