1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun harbe mahara da dama a Nijar

Zulaiha Abubakar
January 10, 2020

Akalla sojoji sama da 20 ne da kuma mahara 63 ne sun rasa rayukansu a Jamhuriyar Nijar sakamakon harin da ‘yan ta'adda suka kai cikin motoci da babura a wani baraki da ke garin Chinegodar a kan iyakar kasar da Mali.

Symbolbild- Nigera - Militärübung
Hoto: picture-alliance/dpa/P. de Poulpiquet

Wani babban jami'in a ma'aikatar tsaro a jamhuriyar Nijar Sulaimane Gazobi ya shaiadwa manema labarai yadda martanin da sojoji suka mayar tare da tallafin jiragen kasar da na abokan hulda ya taimaka wajen korar ‘yan ta'addan tare da nasarar harbe 63 daga cikinsu. Wannan dai shi ne hari na farko da ‘yan ta'addan suka kai a cikin wannan sabuwar shekara ta 2020.