1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Azumi cikin dokar hana cunkoso a Nijar

Salissou Boukari LMJ
April 24, 2020

A Jamhuriyar Nijar a wannan Jumma'ar al'ummar kasar sun dauki azumin watan Ramadan, a daidai lokacin da kasar ke cikin dokar hana haduwar jama'a a Masallatai domin yin jam'in salloli saboda cutar Coronavirus.

Religion und Ramadan in Burkina Faso
Annobar Coronavirus ta tilasta hana yin jam'i a Masallatai Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Kafin zuwan watan azumin dai, al'ummar Jamhuriyar ta Nijar sun tsammaci za a sassauta matakan da aka dauka domin kariya daga Coironavirus din,  musamman ma ganin yadda sannu a hankali masu kamuwa da cutar raguwa a kasar, koda ya ke a wasu lokutan adadin kan karu. Ganin cewa yaune al'ummar Jamhuriyar ta Nijar ta bi sahun sauran kasashe wajen tashi da azumin watan Ramadan din, wanda a cikinsu ake yawaita ayyukan ibada muamman ma salloli da addu'o'i da tafsirai.
Sau tari dai an sha samun dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da sauran al'umma masu neman yi wa dokar zaman gidan karan tsaye, alhali kuma su kansu malaman addini sun yi kira da a nesanci yin zanga-zanga ko fito na fito da hukuma musamman ma a wannan lokaci na azumin watan Ramdan.

Adawa da hana salla a Masallatai a NijarHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Fatan kawo dauki da gyara

Imam Ustaz Aboubakar Ibrahim limamin Masallacin Jumma'a ne, ya ce fatansu shi ne ganin an duba wannan lamari na Masallatai tare da saka cikakken tsari a cikinsu. A wani taron manema labarai da ya kira a wannan Juma'ar, jagoran kungiyoyin fararen hula Nouhou Arzika ya yi kira ga magabata da su rinka daukar matakai na sassauci ga jama'a kamar yadda aka yi kan batun takaita zirga-zirga, tare yin kira ga jama'a da su dukufa ga yin addu'o'in fatan kawo karshen wannan masifa, tare da fatan ganin an sallamo abokansu 'yan kungiyoyin fararen hular da aketsare da su, domin su yi azumi cikin iyalansu.