1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakala a ma'aikatar tsaron kasa kan sayen kayakin soji

Salissou Boukari MNA
February 27, 2020

A karon farko gwamnatin Nijar ta fidda sanarwa kan batun sama da fadin da aka yi a ma’aikatar tsaron kasar dangane da wasu kudade da suka shafi sayen kayayakin aikin sojoji.

Niamey Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Petesch

Cikin daren ranar Talata minista mai magana da yawun gwamnati ya fito ta gidan talabijin na kasa inda ya karanta sanarwar ta gwamnati wadda ta ce dangane da cecekucen da batun bincike da aka yi a ma'aikatar tsaro ta kasa, gwamjnatin Nijar ta yi niyyar kawo haske cikin wannan lamari. Gwamnatin ta ce samar wa sojojin kasar kayayyakin aiki da inganta halin rayuwarsu shi ne abin da ta sa a gaba, kuma sanarwar ta kara da cewa, a tarihin kasar babu wata gwamnati da ta taba samar wa sojojinta kayayakin aiki masu inganci kamar wannan gwamnati, wanda hakan ya sanya sojojin kasar suka zama na misali a cikin takwarorinsu na kasashen Afirka. Kuma dangane da sakamakon biciken da aka yi a cewar Minista Abdourahamane Zakariya gwamnati ta dauki matakai.

"Gwamnati ta yi niyyar ta sa a biya kudaden da aka dauka ba bisa ka'ida ba ko ta hanyar kara farashi kan wata odar kayayyaki, ko kuma an karbi kudi ba a kawo kayayyakin ba, ko an bada rabi da rabi, gwamnati ta nemi da a mika duk wanda bai mayar da kudadan da ya ci ba ta hanyar gaskiya ba ga kotun da ta dace. Sannan za a dauki hukuncin da ya dace ga ma'aikatan gwamnati da ke da hannu cikin wannan badakala, sannan za a kawo gyara wajen dokokin bayar da kwangila a ma'aikatar tsaro ta kasar ganin cewa sabili da dalillan na sirri ba a bayyana ainihin kudaden da ake kashe wa wajen odar kayayyakin na tsaro ba. Shugaban kasa da Firaminista za su bi sau da kafa dan ganin an ci gaba da ayyukan da aka soma na yaki da al'mundahana da dukiyar kasa."
 

Gommai na sojojin Nijar suka mutu a wani hari da 'yan ta'adda suka kai musuHoto: DW/S. Boukari

Sanarwa dai ta haifar da babban cecekuce a tsakanin 'yan Nijar da suke ganin ta dalilin cuwa-cuwa da aka yi ne mai yuwa aka samu mutuwar sojojin Nijar da daman gaske sakamakon hare-haren 'yan ta'adda wanda na baya-bayan nan su ne na Inates da Chinagoder da suka yi sanadiyyar mutuwar sojoji kusan 200. To ko mene ne masana harkokin shari'a suka gani dangane da wannan sanarwa? Docta Amadou Boubakar Hassane masanin dokokin kundin tsarin mulki ne a Jamhuriyar Nijar.

"Da dama dai na zargin cewa gwamnatin ta yi wannan sassauci ne domin akasarin wadanda aka bai wa kwangilar mutanenta ne ko kuma 'yan jam'iyyarta ne."

A halin yanzu dai 'yan siyasa na bangaran masu mulki ko na adawa ba su fito karara suka sanar da matsayinsu dangane da almundahanar da ministan tsaron kasar da kanshi ya sanar da muninta ba, inda ma ya ce hukunci mai tsanani ne ta kamata ga wadanda aka samu da laifi.

Kudaden dai a cewar sanarwar yawansu ya kai biliyan dubu da miliyan 700 na CFA da suka shafi sayan kayayakin aikin sojoji.