Bazoum ya ba da jinisa ga mabukata a Nijar
June 14, 2022Hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai, ta kebe ranakun 14 ga watan Yuni na kowacce shekara domin bayar da tallafin jinin ga marasa lafiya da ke bukatar jini. Sai dai har yanzu a kasashe da dama musamman na Afirka, ba kasafai ake samun masu bayar da jinin yadda ya kamata ba. Misali jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, ta kassance guda daga cikin jihohin kkaasar da ake fuskantar karancin masu bayar da tallafin jinin. Koda yake idan aka akwatanta da sshekaru bakwai din da suka gabata, ana iya cewa an samu karuwar maasu bayar da gudunmawar jinin ga asibitoci da mabukata a jihar ta Maradi.
A wannan karon, domin bayar da tasa gudunmawar da kuma zama abin koyi ga al'ummar da yake mulka, Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar ta Nijar ya kasance cikin masu bayar da jinin ga mabukata. Sau tari dai wasu kan yi zargin cewa, ana sayar da jinin da suke bayarwa gudunmawa a asibitoci. A cewarsu wannan dalili na zaman guda daga cikin abin da yake sanya mutane yin dari-dari wajen bayar da gudunmawar jininsu, sai dai shugaban bankin adana jini na jihar Maradi Malam Mamane Aminu Brah ya musanta wannan zargi. Kungiyar matasa masu hangen nesa dai, na zaman guda daga cikin kungiyoyin da ke bayar da taimakon jini a jihar ta Maradi. Kungiyar na kuma wayar da kan al'umma kan mahimmancin bayar da gudunmawar jinin ga mabukata.