Rantsuwar kama aikin Bazoum a Nijar
April 2, 2021Talla
A yau ne aka rantsar da sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar, bayan cikar wa'adi biyu na shekaru 10 da tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya kwashe ya na jagorancin kasar. Bazoum Mohamed ya zama zababben shugaban kasa bayan da kotun tsarin mulki ta tabbatar masa da nasara, a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.
Bikin shan ratsuwar dai ya samu halartar shugabannin kasashe dabam-dabam na duniya da kuma jami'an diplomasiyya na ciki da wajen kasar. Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar, inda wata gwamnatin farar hula ta mika mulki ga wata gwamnati ta farar hula.