Farar hula sun hallaka sakamakon hare-haren 'yan ta'adda
June 26, 2019Talla
Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce akalla mutane 140 ne suka hallaka a tsakanin watanni biyar na farkon wannan shekara a yankin Diffa sakamakon hare-haren mayakan ta'addancin Boko Haram da ke shigowa yankin daga makofciyar kasar tarayyar Najeriya. Rahoton na hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya ce mutanen da suka hallakan daga farkon wannan shekarar zauke yanzu, sun zarta adadin wadanda suka hallaka a shekarar 2018.