1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude kan iyakokin Nijar da wasu kasashe

Zainab Mohammed Abubakar
August 2, 2023

Sabuwar gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sake bude kan iyakokinta ta kasa da sararin samaniya da wasu kasashe da ke makwabtaka guda biyar.

Coup aftermath in Niger
Hoto: Balima Boureima/REUTERS

Kakakin gwamnatin sojin a wani jawabin da yayi ta gidan talabijin na kasar ya ce, an sake bude hanyoyin shiga kasashen Mali da Burkina Faso da Algeria da Libya da kuma Chadi. Sai dai iyakokin Nijar da Benin da Najeriya, wadanda dukkansu mambobin kungiyar habaka tattalin arzikin yan kin na ECOWAS ne, za su ci gaba da kasancewa a rufe.

A yanzu haka dai tawagar kungiyar ta ECOWAS mai wakilan kasashen 15, karkashin jagorancin Najeriya na ziyara a Niamey domin tattaunawa da shugabannin da suka yi juyin mulki, in ji kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah.

A wannan Laraba(2.08.2023) ce hafsoshin tsaro na kungiyar kasashen yammacin Afirka ke taro a Abuja babban birnin Najeriya, domin tattaunawa kan yadda za a mayar da martani kan juyin mulkin da aka yi a Nijar a makon da ya gabata wanda ya haifar da fargabar barkewar rikici a yankin Sahel na yammacin Afirka.