1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bukatar tallafa wa jihar Diffa da abinci

Abdoulaye Mamane AmadouI/AHJuly 28, 2016

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar Jihar ta Diffa mai fama da rikicin Boko Haram da kuma Jihar Tilabery na fuskantar barazanar yunwa.

Afrika Dürre
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Hukumomin a Jamhuriyar Nijar sun yi wata ganawa da kungiyoyin agaji na kasa da kasa da kasashe masu hannu da shuni, kan tsananin bukatar agajinsu dangane da barazanar fuskantar karancin cimaka kafin nan da karshen watan Disamba a cikin wasu Jihohin kasar.

Tashin hankali Boko Haram ya janyo karancin abinci a Jihar Diffa

Hukumar abinci ta Majalisar Dunkin Duniya PAM ta bayyana tsananin wannan bukatar ta hanyar gwamnatin Nijar don agaza wa jama'a musamman ma a yankin Diffa mai fama da tashin hankali na Boko Haram da yankin Tillabery, inda har yanzu 'yan gudun hijira daga arewacin Mali suke jibge kuma suke fuskantar barzana ta karancin abinci.

Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Jama'a na cikin wani mawuyacin hali na rashin abinci

Babban makasudin taron na hukumomin agajin kasa da kasa da ma tarin kasashe masu hannu da shuni da gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar. Shi ne na daukar matakan kariya a cikin gaggawa kan yiwuwar samun karancin abinci musamman ma a wasu yankunan kasar da ke fama da matsaloli kamar Jihohin Diffa da Tillabery. Duba da barazanar karancin kudaden tafiyar da aiyyukan samar wa jama'a masu tsananin bukata cimaka da hukumar ta majalisar Dunkin Duniya reshen Nijar ta bayyana.

Hoto: Getty Images/AFP/O. Omirin

Duk da kokarin da hukumar ta yi na bayar da agaji ga yara masu matsalar tamowa sama da dubu 800 da wasu tarin dalibbai 'yan makarantu fiye da dubu 200 daga farkon wannan shekarar zuwa watan Yunin da ya gabata.