Ana fama da cutar sankarau a Damagaram
January 6, 2021Talla
Cutar ta bulla ne a tsakiyar watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2020, kuma tuni kimanin mutane 337 suga kamu, kana ta lakume rayukan mutane 12. To amma a cewar Dakta Abu Yahaya da ke zaman shugaban hukumar kiwon lafiyar yankinz, ya nunar da cewa bullar cutar a wanan lokaci akwai ban mamaki. Hukumomin lafiyar dai sun dauki matakin kafa sansanin killace wadanda suka kamu da cutar domin ba su kulawar da ta dace.
An dai hana shiga sansanin domin dakile yaduwar cutar ta sankarau. Shugaban hukumar kiwon lafiyar yankin Dakta Abu Yahya ya kuma tabbatarwa da manema labarai cewar tuni suka kaddamar da alurar rigakafin cutar ga yara daga shekara daya zuwa shekaru 15 a garin Geza Mahaman, inda za a ci gaba da gudanar da ita a sauran garuruwan.