1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojin Nijar da Burkina Faso sun halaka ‘yan ta’adda 100

Gazali Abdou Tasawa ZUD
April 26, 2022

Sojojin Nijar da na Burkina Faso na shan jinjina bayan da suka kashe 'yan ta'adda 100 ba tare da tallafin sojojin Kasashen Yamma ba. Wasu 'yan Nijar sun ce wannan manuniya ce ga karfin da sojojinsu ke da shi.

Nigeria Soldaten in Diffa Aktion gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/J. Penney

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta Nijar ta bayyana cewa farmakin sharar daji da aka yi wa lakabi da  ‘Operation TAALI 3‘, ma’ana hadin kai a cikin harshen Gurmanci, wanda suka kaddamar da hadin gwiwa da takwarorinsu na makwabciyar kasa Burkina Faso a tsawon makonni uku kan iyakar kasashen biyu ya ba su damar halaka ‘yan ta’adda kimanin 100 kana suka kama wasu mutanen akalla 40 da ake zargi da yi wa mahara leken asiri. Kazalika sojojin kasashen biyu sun wargaza wasu cibiyoyin kera makamai da ma tarwatsa wani sansanin ‘yan ta’addan tare da kama tarin makamai da albarusai. Akwai ma  gwamman galan-galan na man fetur da motoci da kuma tarin haramtattun kwayoyi da jami’an tsaron suka kama.

Sojojin NijarHoto: Reuters/J. Penney

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Tournons La Page Nigermai adawa da girke sojojin ketare a Nijar, Moudi Moussa, ya ce nasarar da aka samu ta tabbatar da matsayarsu na cewa sojojin Nijar za su iya cin galaba kan ‘yan ta’adda ba tare da jibge sojojin ketare ba.

 ‘‘Darasin da ya kamata a dauka kamar yadda Shugaban kasa Bazoum ya fadi da farko, ba ma bukatar sojoji a kasa. Muna bukatar kayan aiki da ba da yarda ga sojojinmu. In aka yi haka, mun yi imani babu wani tashin hankali da zai tunkaro mu ba tare da sun iya magance mana shi ba“ in ji Moussa.

 

Shugabannin sojojin kasashen biyu sun girke sansaninsu ne a garin Dori na Burkina Faso, inda daga nan ne suka yi aiki kafada-da-kafada wajen tsara wannan farmaki, wanda aka yi amfani da daruruwan sojoji daga kasashen biyu da jiragen leken asiri da kuma na yaki.

Sojojin Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

‘Yan Nijar sun jinjina wa sojojin kasarsu

Wannan nasara da sojojin kasashen biyu suka yi a cikin wannan farmaki ta dau hankalin jama’a a kasar ta Nijar wadanda suka yaba wa sojojin. Wani dan kasar mazaunin birnin amai ya shaida wa DW cewa ‘‘Wallahi abin da sojojin kasashen suka yi ya yi kyau. Ina ma a ce ita ma Mali ta shigo, ta hade da Nijar da Burkina Faso wurin yakar  ta’addanci...’’  

Wasu ‘yan Nijar dai na ganin idan da Mali za ta hada hannu da kasashen biyu da kasashen sun ci dunun matsalar tsaron da ke addabar iyakokinsu.