SiyasaAfirka
Nijar da Najeriya sun kashe 'yan ta'adda
May 30, 2023Talla
Rundunar sojin Nijar ta ce ta yi nasarar halaka akalla mayakan jihadi hamsin da biyar a yayin wani samame na hadin gwiwa da ta kai da taimakon rundunar sojin Najeriya a mabuyar 'yan ta'addan ISWAP. Rundunar ta yi karin bayani da cewa, an kwashi kwanaki 22 ana kai farmakin kan mabuyar 'yan ta'adda a garin Arege a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ke kan iyaka da Nijar.
Kasashen biyu da ke fama da matsalar masu tayar da kayar baya sun kai samamen ne, don kara matsin lamba ga kungiyar da kuma yanke mata hanyoyin samun kayayyaki. Nijar na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da tashe-tashen hankula a sakamakon ayyukan 'yan ta'addan.