Kasuwancin dalibai a Nijar domin rage radadin rashi
October 26, 2023![](https://static.dw.com/image/65939278_800.webp)
Talla
A Jamhuriyar Nijar, dubban daliban jami'a ne ke yin sana'o'i ko ayyukan hannu a wani matakin ragewa uwayensu nauyi na dawainiyar da suke musu duba da yanayin da kasar ke ciki, abin da ke taimakawa wajen rage radadin da ake cikinsa a Nijar na takunkunin karya tattalin arziki da ECOWAS ta saka wa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.