1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Damuwa kan yawan mutuwar aure

October 6, 2023

A sakamakon damuwa kan yawan mutuwar aure kungiyoyin agaji kamar CRS sun bude makarantu domin koyar da ma'aurata maza da mata hidimar rikon iyali.

Niger Bilma Salz
Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP

.

A fanin kula da lafiyar iyali a cewar Nanziru Manzo magidanta na taka rawa ka tafi da iyalan ka ka kaisu asibiti, ka ga wane irin aiki aka yi kowa ka bashi hakinsa da wannan makaranta ta zo ta ma'aurata mun ga sauyi sosai da sosai za ka ga ko da yaushe kuna tattaunawa kana jin dadi suna jin dadi.

Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

A yayin da magidanta maza suka bayyana irin aikace aikacen da suke dafa wa matansu,ko wadane gudumawa matan ke bayarwa ga magidantan?  

To sai dai a cewar Saratu Lukuma sun ga bambanci da rayuwarsu ta baya da idan aka yi aure tsakanin mace da miji soyayya daga dandali ta kare, idan aka zo gida sai fada amman yanzu da aka samu makarantar ma'aurata komi yayi dai dai ba wata hayaniya kana girki yana taimaka maka kuna tafiya da fira zama tare abinci tare .   

Nijar Maradi: Maigida da IyalansaHoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

To ko yaya hararu Musa malamin dake jagorantar waye kan ke fassara waye kan. Ita kanta makarantar tana nuna mana yadda za ka tsara iyalanka bayan wannan kuma akwai yadda ake nuna mana yadda ake jagoranci da warware matsaloli idan sun faru yadda, bayan wannan akwai yaki da bangaren tamowa da muke koya wa dalibai wadanda in suka bi wannan mataki za su yaki tamowa .

A cewar mazauna garin hatta da yawan kai kara gidan mai gari ya rageu tsakanin ma'aurata ba wai  mutuwar aure ba.