1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisa sun amince da gyaran albashinsu

Gazali Abdou Tasawa
November 23, 2022

'Yan majalisar dokokin Nijar sun kada kuri’ar amincewa gyaran fuskar da suka yi wa dokar kudaden alawus da albashinsu.

Majalisar dokokin Nijar
Majalisar dokokin NijarHoto: Gazali A. Tassawa/DW

'Yan majalisar sun yi wa dokar kudaden alawus din nasu gyaran huska ne domin fitar da wasu kurakurai da ta kunsa. Sai dai wasu kungiyoyin fararen hula na kasar sun zarge su da daukar kudaden alawus da dama ba a kan ka'ida ba.

Da kuri'u 151 ne dai 'yan majalisar dokokin kasar na bangaren masu mulki da na bangaren adawa da suka halarci muhawara suka kada kuri'ar amincewa da gyaran huskar da suka yi wa dokar da ta tsara kudaden alawus da na albashin ‚yan majalisar dokokin kasar ta Nijar. Honnorable Kalla Moutari shugaban kwamitin majalisar da ya gabatar da dokar ya ce sun yi wa dokar alawus din gyaran huska ne domin magance wasu kusu matsaloli da ta kunsa a daidai loakcin da a karon farko ake shirin yi wa majalisar dokokin kasar bincike.

Shugaban kwamitin majalisa Kalla Moutari Hoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

Sai dai tuni wasu kungiyoyin farar hula na kasar ta Nijar suka soki lamirin majalisar dokokin kasar ta Nijar wacce suke zargi da fakewa da gyaran huskar domin kara wa kansu kudaden alawus ba a kann ka'ida ba. Malam Nouhou Arzika na kungiyar MPCR na dag cikin masu wannan zargi.

To amma da yake mayar da martani Kalla Moutari ya ce zargin da ake yi masu bashi da tushe domin gyaran Fuskar da suka yi wa dokar bai tanadi karin ko da dala daya ba ne na alawus ga 'yan majalisar.

Nouhou Arzika na kungiyar MPCR Hoto: DW/T.Mösch

Sai dai a bahasin da suka gabatar a lokacin mahawarar, da dama daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ta Nijar sun bayyana bukatar ganin a shekaru masu zuwa an kara kudaden alawus da na albashin 'yan majalisar dokokin nijar wanda suka ce a yanzu shi ne mafi karanci a cikin kasashe 15 na kungiyar ECOWAS.