1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban jama'a sun amsa kiran kungiyoyi a Nijar

Salissou Boukari
September 9, 2018

Watanni shida bayan da hukumomi ke hana gudanar da zanga-zangar kungiyoyin fararan hulla, gamayayyar kungiyoyin fararan hullan da 'yan siyasa sun samu gudanar da zanga-zangar gami da taron gangami a birnin Yamai.

Niger Protest gegen das Haushaltsgesetz der Regierung
Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Dubban jama'a ne dai suka amsa kiran kungiyoyin fararan hullan, wadda kuma wannan ita ce zanga-zanga ta farko da suka shirya tun bayan da aka sallamo su daga gidajen kaso daban-daban bayan wani kamu da aka yi musu na tsawon watanni sakamakon yin wata zanga-zangar da hukumomi suka haramta.

Rahotanni na cewa a wurin wannan baban taron gangami na birnin Yamai, baya ma ga jagororin kungiyoyin fararan hullan, an samu halartar shugaban jam'iyyar MPN Kishin Kasa Ibrahim Yacouba, wanda a watannin baya jam'iyyarsa ta  fice daga gamayyar jam'iyyun da ke mulki a kasar ta Nijar.

Masu zanga-zanga sun soki lamirin mahakumatan kasar ta Nijar, musamman ma kan yadda suka yarda aka girka sansanonin sojojin kasashen waje a kasar, da kuma yadda hukumomin ke tafiyar da lamuransu na mulki.

A jihar Diffa ma da ta yi fama da rikicin Boko Haram an gudanar da zanga-zangar, inda cikin kulawa ta jami'an tsaro masu zanga-zangar suka isa har wajen hukumomi inda suka mika kokensu.