1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ECOWAS za ta tattauna da sojojin Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 10, 2023

Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kaksashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da jagororin juyin mulkin Nijar kan batun mika mulki hannun farar hula cikin takaitaccen lokaci.

Najeriya | ECOWAS | CEDEAO | Najeriya | Taro | Nijar
Taron kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a Najeriya kan Jamhuriyar NijarHoto: Kola Sulaimon/AFP

Wannan dai na kunshe ne cikin taakardar bayan taro da kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta kammala a Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya, inda suka sanar da dora alhakin tattaunawa da shugabannin gwamnatin sojan da suka kifar da gwamnatin farar hula karkashin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum na Nijar kan shugabannin kasashen Togo da Saliyo da kuma Jamhuriyar Benin.

Tun da fari Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya kana jagoran kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, ya bayyana cewa kungiyar za ta yi duk mai yiwuwa domin tallafawa kasashen yankin da ke karkashin jagorancin soja da ma sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen wajen ganin sun koma kan turbar dimukuradiyya. Sai dai duk da haka kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta yi gargadin cewa, in har sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din suka ki bayar da hadin kai ga wannan kwamiti to tabbas takunkumin kungiyar zai ci gaba kuma akwai yiwuwar yin amfani da karfin soja wajen tabbatar da dawo da mulkin dimukuradiyya a kasar.