1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ginin otel zai lashe makudan kudi a Nijar

Gazali Abdou Tasawa
August 5, 2021

Wani rukuni na 'yan majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, ya aikawa shugaban majalisar dokokin kasar wasika domin neman ya dakatar da aikin wani katafaren gini da wasu ke cewa otel ne ake shirin ginawa a cikin majalisar.

Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Yin gini mai hawa hudu a cikin majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, ya janyo cece-kuceHoto: DW

Matakin 'yan majalisar da yawansu ya kai 40 dai, ya biyo bayan korafe-korafe da aka fara samu daga 'yan kasar, kan rashin dacewar ginin da ake ganin zai lakume kudi kimanin miliyan dubu 15 na CFA a daidai lokacin da Nijar din ke fama da talauci. A cikin wasikar 'yan majalisar dokokin da suka fito daga bangaren masu mulki da kuma na adawa, sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda majalisar dokokin ke shirin aiwatar da wannan aiki a cikin duhu ba tare da akasarin 'ya'yanta sun san abin da za a gina kuma kan wane dalili za ai ginin ba, bare kuma ayi batun sauran talakawan kasar. Makonni da dama kenan dai da shiri na yin wannan gini mai hawa hudu a majalisar dokokin kasar, ke shan suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta MPCR a Jamhuriyar Nijar, Nouhou ArzikaHoto: DW/T.Mösch

Akan haka ne kungiyar MPCR ta Malam Nouhou Arzika ta jinjinawa 'yan majalisar kan matakin suka dauka. Wannan aiki da majalisar dokokin ke shirin yi dai na cike da rudani, inda wasu bayanai ke cewa wani katafaren otel ne ake shirin ginawa 'yan majalisar yayin da wasu ke cewa ofisoshi ne za a ginawa kwamitocin majalisar. Sai dai ko ma me  majalisar dokokin ke shirin ginawa, Malam Nouhou Arzika na kungiyar MPCR ya ce suna zargin akwai alamar cin hanci da rashawa a ciki. Kawo yanzu dai shugaban majalisar dokokin ta Nijar Alhaji Seini Oumarou wanda ba a karkashin shugabancinsa ne aka bayar da kwagilar aikin ba, bai kai ga bayar da amsar wasikar 'yan majalisar ba. Yanzu haka dai al'ummar kasar sun zura idanu su gani ko zai amince da bukatar takwarorin nasa da ma wasu 'yan kasa, ko kuma  zai ce baki alkalami ya riga ya bushe.