1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwagwarmayar siyasa a Nijar shekaru 60 da samun 'yancin kai

Mahaman Kanta MNA
August 3, 2020

Rikita-rikitar siyasa ta hana Jamhuriyar Nijar samun wani ci-gaba na a zo gani shekaru 60 da samun 'yancin kanta daga kasar Faransa.

Demokratische Republik Kongo Kinshasa | Nigerianischer Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Presidence RDC/G. Kusema

A jamhuriyar Nijar ranar 3 watan Agusta shekaru 60 daidai da kasar ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar kasar Faransa, amma duk wadannan shekarun kasar ta yi ta fama da rikita-rikitar siyasa wadanda suka taimaka wajen hanata ci-gaba.

Bayan yadda aka ga mulkin magabatan farko da suka karbi mulkin daga Turuwan mulkin mallakar na kasar Faransa, bisa ga jagorancin shugaban kasar Nijar na farko marigayi Alhaji Diori Hamani, yau shekaru 60 daidai, duk da cewa a lokacin kasar ba ta da hali, amma saboda akidar kishin son kasa da wadancan magabatan suke da, sun yi ayyukka da dama masu kyau da ya kamata mahukuntan yanzu su yi koyi da su.

Kamar a sauran kasashen Afirka a Nijar ma batun siyasa na daukar hankalin jama'a sosaiHoto: picture-alliance/dpa/EPA/A. Gillis

Bayan kadawar iskar canji a duniya a 1991 da aka samu kafuwar jam'iyyu barkatai, a maimakon a shiga karnin ci-gaba ba a yi amfani da wannan damar ba, sai rikitan siyasa a cikin kawancen da shugabannin jam'iyun suke kallawa. Abin da ke sa tarnaki wajen ci-gaban kasa da kuma hada kan al'umma.

Nassirou Saidou shugaban wata kungiyar farar hula davke rajin kare dimukuradiyya da ake kira Muryar Talaka, manazarci kan al'amuran yau da kullum ne, ya ce a Nijar idan jam'iyyun siyasa suka kulla kawance za ka ga suna wa juna zagon kasa. Yawanci manyan jam'iyyu suke hakan, inda suke ta shisshigin tarwatsa abokan kawancensu ko su kirkiro wasu mutanen da za su yi tawaye cikin jam'iyyun daga nan jam'iyyun su wargaje.

Amma a cewar Mahamadou Asoumana kakakin jam'iyar PNDS Tarayya da ke mulki, wannan rikicin kawancen da ake yadawa a cikin wannan mulkin na shugaba Mahamadu Issoufou, duk jami'yyun da suka kulla kawance har yanzu babu wata matsala da ta samu tsakaninsu, suna zaune tare lafiya.

Hama Amadou shugaban jam'iyyar adawa ta Lumana AfrikaHoto: Imago/W. Prange

Sai dai a nasu wajen bangaren adawa sun dangata wannan rikicin da rashin son a yi zabe na gaskiya, wanda suka dorama masu mulki hakkinsa, kamar yadda Maidouka Abouba, wani jigo a jam'iyyar Lumana Afrika ta Hama Amadou madugun adawa ya ce masu mulkin ba sa son su tsara zaben da talaka idan ya saka kuri'arsa, ta je inda ya zaba.

A cewar Nassirou Saidou 'yan siyasar Nijar ya jam'iyya ba su da akida da alkibla shi ya sa kowace jam'iyya take kulla kawance da kowace domin ba yadda za a yi 'yan gurguzu su hadu da 'yan jari hujja. Amma Nijar babu wannan kishin illa a hadu a cimma rarraba madafun iko su ko talakawa iyakacin ranar zabe su saka kuri'a daga nan an manta da su.

Wannan rikicin kawancen a cikin jam'iyyun da ke mulki, an sha kokarin rufe shi, amma sai da ya baiyana kowa ya san irin zaman da ake ciki. Haka can bangaren adawar ma ba sa rasa matsala saboda ba su da mulki ne ba ka jin motsin komai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani