Nijar: Hari bisa kuskure kan fararen hula
October 28, 2025
Bayanai daga yankin Abalar Filigue na Tillabery sun tabbatar da afkuwar lamarin wanda suka ce ya wakana ne a wani kauye mai suna Tchimbarkawa inda jirgin maras matuki da ake kyautata zaton na rundunar sojin Nijar ne ya kai hari a bisa kuskure a kasuwar kauye inda ya halaka mutane da dama a yayin da wasu da dama suka jikkata kamar dai yadda wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa DW
Sai dai sashen kula da tsanwan layin waya na hulda da manema labarai na rundunar soj Nijar ya tabbatar da kai harin wanda ya ce sun kai shi ne a kan ‘yan ta'adda inda suka halaka da dama. To amma Malam Sahanin Mahamadou mai adawa da mulkin soja a Nijar ya ce akwai bukatar gwamnati ta gudanar da bincike a kan lamarin.
Sai dai wasu ‘yan Nijar na danganta wannan hadari da yadda mazauna wasu yankunan da ke fama da matsalar tsaro basa mutunta dokokin da mahukunta suka dauka don kare farara hula a fagen yaki da ‘yan ta'adda.
Yanzu dai 'yan kasa sun kasa kunne suna sauraran fitowar sanarwa daga rundunar domin sanin takamaiman abin da ya wakana a kauyen na Chimbarkawa na jihar Tillabery. Ko a watan Satumban da ya gabata wani jirgi maras matuki na sojin Nijar ya kai hari a bisa kuskure a kasuwar kauye mai suna Injar a Jihar Tillabery inda ya halaka fararen hula da dama.