1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An hallaka soja hudu a yankin Diffa

Abdoulaye Mamane Amadou
April 5, 2021

A yankin Diffa da ke Kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar 'yan bindiga sun kai tagwayen hare-haren ta'addanci tare da kisan sojan kasar hudu a karshen makon jiya.

Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A wata sanarwar da ta fitar a yammacin jiya Lahadi, ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta ce ko baya ga mutuwar sojojin hudu, tagwayen hare-haren kan mashigar sojanta da ke N'Gagam da PK5 a gundumar Diffa, sun raunata wasu soja shida a yayin da kawo yanzu wani daya sojan ya yi batan dabo.

Sai dai sanarwar ta kuma kara da cewa askarawan sojan kasar, sun yi nasarar hallaka mayakan da dama tare da lalata manyan muggan makamai ta hanyar luguden wuta ta sama.

Wannan harin dai na zaman irinsa na farko kenan da mayakan 'yan ta'adda suka kaddamar a kasar, jim kadan bayan karbar rantsuwar fara aiki da sabon shugaban kasar Mohamed Bazoum ya yi a karshen makon jiya.