1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Harsunan uwa a makarantun boko

Abdoulaye Mamane Amadou
November 7, 2017

A wani yunkuri na shanyo kan matsalolin komabayan ilimi a makarantun boko na kasar, hukumomin kasar sun shigar da tsarin koyarwa a cikin harsunan gida a makarantun bokon daga matakin farko.

Schule in Niamey
Yara 'yan makaranta masu daukan darasi da harsunan uwa a birnin Yamai na NijarHoto: DW/A. Mamane Amadou

Wannan dai shi ne karo na farko da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sake dawo da wannan tsari bayan kaddamar da shi a shekarar 1973 shekaru 40 kenan da suka gabata . Makarantar Firamare da ke unguwar Lazaret a Yamai babban birnin kasar na daya daga cikin makarantun na farko da aka soma aiki da wannan sabon tsari na koyarwa a harsunan gida.

Madame Mariatou Abdou Malamar koyar da Hausa a Ecole Lazaret birnin YamaiHoto: DW/A. Mamane Amadou

 Mme Roua Boukar Koura babbar jami'ar kula da shigar da tsare-tsare a makarantun bokon kasar ta Nijar ta ce:"Yaron da aka karantar da shi da harshen uwa ya fi koyon karatu da kwarewa da kuma gane baki na karatun fiye da wanda ake koyarwa da harshe na waje."

A makaranta da ake kira "Ecole Hausa" da ke karamar hukuma ta biyu ta birnin Yamai wata malama mai suna Rabiatou Abdou na daga cikin maluman koyar da harshen Hausa, wadda ta ce da ta gamsu da yanda dalibanta 'yan aji na biyu ke kara kwarewa wajen karatu da rubutu:"Yara na fahimta saboda cikin harshensu ne ake koyar da su. Kamar yanda idan sun koma gida suke magana da iyayensu, hakan kuma a nan muke koyarsu da wannan harshe. To wannan abin na taimaka mana sosai wajen ganin an samu saukin karatu."

Dan makaranta Abdoulwahab na karanta hausa a makarantar bokoHoto: DW/A. Mamane Amadou

Yaran dai idan suka fice zuwa mataki na gaba zuwa ajinsu na uku za su rinka hadawa da harshen Faransanci don kara gogewa, Sai dai duk da wadannan sauye-sauye sauye wasu iyayen yara sun nuna tsananin damuwa game da sabuwar fasahar kaman yadda Malam Salissou Abba wani mazaunin unguwar Poudriere a birnin na Yamai na yi tsokaci:

"A ganina wannan tsarin baida wani tasiri domin gani nake tamkamar wani koma baya ne don a cikin harshen turanci ma an kasa ganewa balantana an koma ga harsuna na cikin gida, saboda hakan a ganina koma baya ne zai dada karuwa a harkar ilimin."Kimanin makarantu boko 5000 ne tsarin ya shafa a fadin kasar ta Nijar, inda a birnin Niamey kadai ake da makarantun fiye da 160 a cikin wasu harsuna uku daga cikin harsuna biyar na uwa da suka hada da Hausa, Zabarmanci, Fulatanci, Barbarci, da Buzanci da tsarin zai mayar da hankali a kan su don samar da ilimi mai inganci.