Nijar: Gwamnati ta soke hutun Ista
November 7, 2024Gwamnatinmulkin sojan kasar ta Nijar ta dauki matakin soke a dokance hutun makon bikin na ISTA ko Paques da maye gurbinshi da hutun kwanaki 10 na karshen azumin watan Ramadan, bayan da sakamakon gwajin wannan tsari da aka yi a shekarar da ta gabata ya nunar da cewa al'ummar Nijar wacce kusan kaso 99 cikin dari Musulmi ne ta bayyana gamsuwarta da shi sosai. Tuni kuma kungiyoyin addinin Islama suka soma bayyana farin cikinsu da tabbatar da hutun karshen azumin watan na Ramadan a hakumance. Cheick Mohamed Alassane babban limamin masallacin Alfarouk a birnin Yamai kana mashawarci a babbar kungiyar addinin Muslunci ta kasa.
''A matsayinmu na Musulmi, wata Ramadan, wata ne mai albarka musamman kwanakinsa 10 na karshe wadanda cikinsu ke da daren Lailatul-Kadari. Su ne kwanakin da Manzon Allah (SAW ) ya yi umurni da a raya su da ibadodi. Dan haka ba da hutu a cikin wannan kwanaki da wannan gwamnati mai albarka ta CNSP ta yi ba karamin farin ciki ne ba ga al'ummar Musulmi, dan su samu damar yin ibadodinsu da sallolinsu na dare a cikin nutsuwa.''
Suma dai Malaman makaranta sun yaba da matakin wanda suka ce sun jima da suna bukatarsa ta la'akari da wahalar da suke fuskanta a cikin aiki a karshen watan azumin na Ramadan. Alhaji Amadou Roufa'I Sallaou shugaban makarantar le Declic mai zaman kanta a Yamai ya ce abin farin ciki ne.