1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Iyalan Bazoum sun maka talabijin RTN a kotu

Gazali Abdou Tasawa
December 18, 2023

Iyalan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum sun maka shugabannin gidan radiyo da talabijin na kasa RTN da kuma jaridar "Nouveau Republicain” a kotu bisa zargi bata masu suna

Niger Mohamed Bazoum
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Gidan radiyo da talabijin na kasa wato RTN ya yi rahoto kan wani labari da jaridar Nouveau Republicain mai zaman kanta ta wallafa a ranar 19 ga watan Oktoban 2023, inda ta zargi hambararren shugaban kasa Bazoum Mohammed da bayar da kwagila ta biliyoyin kudaden CFA ga iyalai da danginsa ba a kan ka'ida ba. Labarin da iyalan hambararren shugaban kasar suka ce sam ba gaskiya ba ne tare da daukar matakin kalubalantar gidan radiyon da talabijin din na kasa da kuma jaridar ta Nouveau Republicain a gaban kuliya kamar yadda Barrister Said Ould Salem Moustapha lauyan iyalan hambarran shugaban kasar ya shaida wa ‘yan jarida.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar gidan radiyo da talabijin din na kasa RTN ya ce shi ruwaito labari ya yi kawai daga wata jarida, a karkashin wani tsari da ya bijiro da shi na tsara jerin rahotanni na fallasa irin muggan ayyukan da suka wakana a gwamnatocin da suka shude ta hanyar kiyaye ka'idojin aikin jarida.

Karin Bayani: Fafutukar yaki da cin hanci a Nijar

Sanarwar ta ce wannan rahoto somin tabi ne daga jerin rahotannin da ya tsara kan yaki da cin hanci da rashawa da dabi'ar amfani da mulki wajen samar da garabasa ga iyalai da dangi da suka wakana a gwamnatocin da suka shude. Tashar RTN za ta ci gaba da kawo hujjoji masu karfi kan batun a bisa taimakon ma'aikatu da kotuna da abokan hulda na waje masu yaki da wadannan dabi'u. Kuma wannan shiri tsari ne wanda tashar RTN ta bijiro da shi da kanta, sabanin danganta shirin da wasu suka fara yi da wata manufa a shafukan sada zumunta

Sai dai daga nashi bangare babban editan jaridar ta Nouveau republicain da ta fara wallafa labarin, ya ce ba za su yi magana ba har sai lokacin da takardar karar ta shigo a hannunsu. 

Rahoton da gidan radiyo da talabijin din na kasa ya hada dai ya haifar da muhawara inda wasu ‘yan kasar musamman masu kusanci da hambararren shugaban kasar suka fara zargin abokan hamayyarsu na cikin gida da hada baki da kafar yada labaran ta gwamnati domin shafa wa hambararren shugaban kasar kashin kaji. 

Yanzu dai ‘yan kasa sun zura ido su ga yadda za ta kaya a gaban kotu tsakanin wadannan kafafen yada labarai da kuma iyalan hambararre shugaban kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani