1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An saki 'yan zanga zangar bayan zabe

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2022

A Jamhuriyar Nijar jama’a na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan matakin da hukumomin shari’a suka dauka na sallamar akasarin mutanen da aka kama a lokacin zanga-zangar bayan zaben da ‘yan adawa suka shirya

Niger - Demonstration gegen den Terror in Zinder
Masu zanga zanga a kasar NijarHoto: DW/L. Hami

A wani taron manema labarai babban mai shigar da kara na gwamnatin Nijar Mai shari’a Chaibou Moussa ya tabbatar da sakin mafi yawancin mutanen da aka kama a lokacin zanga-zangar ‘yan adawa ta bayan zabe wacce ta rikide zuwa tarzoma a cikin birnin Yamai 

"Yace a lokacin da suka fara wannan bincike an kama mutane da yawa kuma an tuhume su da laifuka masu yawa da suka hada da kona gidajen mutane da hanyoyi da shagunan 'yan kasuwa da kashe mutane da cin zarafin wasu. Ana ci gaba da bincike kuma aiki na tafiya daidai. Wadanda ba su da laifi ana nan ana sakinsu. Wadanda laifinsu babba ne ana rike da su ana ci gaba da zurfafa bincike kamar yadda doka ta tanada. Wadanda doka ta ce a gurfanar za a gurfanar da su. Wadanda ta ce a sake su za a sake su. Kuma mutane da suka rage a tsare ba su wuce  mutum 30 ba daga cikin daruruwa da aka kama wanda ke nufin aikin na tafiya yadda ya kamata"

Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Kamen na wancen lokaci dai ya ritsa da wasu manyan 'yan siyasa da suka hada da jagoran jam‘iyyar adawa ta Lumana Afirka Malam Hama Amadou da Janar Moumouni Boureima mai ritaya da Abdou Maman Lokoko shugaban jam’iyyar MPP Munatare, da ma wasu ‘yan fafutuka irin su Anas Djibrilla. Shugaban jam’iyyar ta MPP Munatare Abdou Maman Lokoko na daga cikin wadanda aka sallama 

"Yace na gode wa Allah da ya sa na fito daga gidan yarin nan lafiya. Na kuma ji dadi sosai da yadda shari’a ta wanke ni bisa zarge-zargen da aka yi mani. Kuma Allah Ubangiji ya sa kaffara ce wannan rikon da aka yi mani. Na fito cikin koshin lafiya domin inda na yi zama ba a kuntata mani ba. Ina fatan sauran mutanen da na baro can Allah ya sa samu su komo cikin iyalansu. Sannan ina fatan ‘yan kasa mu fahimci juna cewa siyasa ba gaba ba ce"


Sai dai Malam Bana Ibrahim matashin dan siyasa a jam’iyyar adawa ta Lumana Afirka kana dan fafutuka na ganin matakin sakin mutanen bayan gurfanar da su a gaban kuliya ba shi ne mataki mafi a’ala ga burin da gwamnatin shugaba Bazoum ke da shi na sasanta ‘yan kasa da hada kansu ba.

Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

"Yace shugaba Bazoum idan yana so ya hada kan ‘yan Nijar, mu a ganinmu afuwa ya kamata a yi wa mutanen nan a sake su. Bai kamata a ce sai an gurfanar da su an yi masu shari’a an yanke masu hukunci kana a sake su ba. Domin kowa ya san a Nijar duk dan siyasar da aka yanke wa hukunci na shekara daya to bashi da damar tsayawa takara, ba a iya zaban shi baya iya zabe"

Wannan mataki na sakin masu zanga-zangar bayan zaben da aka kama na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Mohamed Bazoum ke shirin cika shekara daya a kan karagar mulki, inda ya dukufa wajen neman hada kan ‘yan kasa domin hada-karfi da karfe wajen tunkarar kalubalan da ke a gaban kasar da suka hada da matsalar tsaro