Nijar: Zaman makoki na kwanaki uku bayan harin Boko Haram
June 7, 2016Ko da yake ba shi ne karon farko da mayakan na Boko Haram ke kaddamar da hare-hare a yankin na Diffa ba, to amma ana iya cewa farmakin na baya bayan nan da mayakan suka kai a garin Bosso ya girgiza 'yan kasar da ma gwamnati, wacce tun daga farko take ikirarin samun nasara kann Boko Haram. Kamarin farmakin dai da shi ne irinsa na farko mafi muni da ake iya cewar kungiyar ta Boko Haram ta yi ya haifar da kiran taron majalisar ministoci na gaggawa a karkashin jagorancin shugaban kasa wanda 'yan kasar suka yi tsammannin zai katse ziyararsa ta aiki da ya kai a kasar Senegal a ranar da aka kaddamar da farmakin.
Hare-haren dai na tun daga ranar Jumma’a sun kuma haifar da rudani inda gwamnati ta bayyana sojanta 30 suka kwanta dama wasu da dama suka jikata. To sai dai taron majalisar ministocin da aka karanta sanarwarsa a kafar yada labaru mallakar gwamnti a ranar Litinin, ya yi wa sakamakon kwaskwarima.
Sabbin alkalumman sojojin da suka rasa rayukansu
Sanarwar bayan taron majalisar ministocin dai ta ce kimanin sojan Nijar 26 ne suka halaka da wasu sojan Najeriya biyu, sannan 112 daga ciki suka ji mummunan rauni, a yayin da 'yan Boko Haram suka yi asarar mutum 55 da raunata da dama daga ciki. Taron ministocin dai ya kuma karyata karbe iko da garin kamar yadda wasu ke cewa 'yan Boko Haram sun yi, kana sanarwar ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki uku.
To ko yaya 'yan kasar suka ji da wannan mataki? Ga dai ra'ayoyinsu:
"Wannan kwana uku na nuna juyayi ba su ne muka fi bukata ba, mun fi son a dauki matakai kwarara don kare 'yan kasa da su ma sojan su kare kansu."
"Ya kamata abin da ya auku kowa ya ji shi ba wai a rinka boye-boye ba kuma a bai wa sojojinmu kayan aiki."
Tuni su ma masu sharhi a kan al’amuran tsaro ke tofa albarkacin bakinsu kan halin da yankin ya tsunduma. Farfesa Issoufou Yahaya wani masanin tsaro ya ce ba tun yau ba suke yi wa gwamnatin Nijar hannunka mai sanda.
"Tun da jimawa muke cewar Nijar a yi hankali domin a Najeriya idan har korarsu ta yi karfi to duk wanda za su yi, za su fito daga kasar su bidi abinci da makamai wajen kasashen da ke makwabtaka da Najeriya kamar su Nijar. Kuma ana lura da cewar kamar damana ta kama tana son ta yi nisa kenan, ya kamata su bidi inda babu ruwa su nemi makamai su nemi abinci don su ajiye har bayan damana. Ya kamata a saka wadanda suka san harkar yaki gaba a ba su kayan aiki, a bar su su yi aikinsu kawai."
Wadata sojoji da makamai da sauran kayan aiki
Sai dai ga wasu masu sharhi ire-Iren su Lawali Abubakar harin na yankin Diffa ba abin mamaki ba ne ganin irin matsin lambar da sojan Najeriya ke saka wa mayakan na Boko Haram.
"Sam ba su da wurin da za su shiga yanzu su nemi abinci ko su kwanta su huta dole sai sun nemi wata kasa ko wani kauye don shi ne suke neman Bosso. Dole sai an tashi haikan an nemi mutane an basu makamai da kayan yaki don su koresu. To akwai wuya don wurin suke neman su samu su yi gurgun zama su fake har su sake yada akidarsu zuwa wasu kasashen kamar su Chadi da Najeriya.
Rahotanni na cewa daukacin jama’ar da aka kiyasta sun kai dubu 50 da suke a garin na Bosso sun kaurace wa jihar a yayin da wasu rahotanni ma suka ce sojan da suke garin sun fice labarin da gwamnati ta karyata.
A wani mataki na magance matsalar dai yanzu hakan shugaban Nijar Mouhamadou Issoufou na wata ziyara a kasar Chadi don ganawa da hukumomin kasar kan matsalar ta Boko Haram da ke neman ta gagari hukumomin Nijar a yankin na Diffa.